News
Sojoji Sun Musanta Kashe Fararen-Hula A Harin Sama Da Aka Kai Kasuwa A Zamfara
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce babu wata kwakkwarar shaida da ke tabbatar da cewa harin saman da ta kai kan ’yan ta’adda a Jihar Zamfara ya yi sanadin mutuwar fararen-hula.
Rundunar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta ce rahotannin da ke ikirarin cewa mutane da dama sun mutu a harin ba su da tabbaci, tare da zargin cewa wasu bayanan na iya kasancewa masu ruɗani.
An Samu Sama Da Mutum 100 Da Ake Zargin Sun Kamu Da Cutar Sankarau A Katsina
Tun farko dai ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta zargi rundunar da kashe akalla fararen-hula 100 a wani harin jirgin sama da aka kai ranar 10 ga watan Mayu a wata kasuwa da ke garin Tumfa a Jihar Zamfara, tare da kira ga hukumomi su gudanar da bincike cikin gaggawa.
Sai dai mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce babu wani bincike na hukuma ko tantancewa mai zaman kanta da ya tabbatar da zargin asarar rayukan fararen-hula.
A cewarsa, an kai harin ne bisa ƙa’idojin dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna akwai wani taron manyan shugabannin ’yan ta’adda a yankin.
“An gudanar da aikin ne kan wani tabbataccen taron shugabannin ’yan ta’adda bayan tattara bayanan leƙen asiri daga mabambantan hanyoyi,” in ji sanarwar.
Onoja ya ƙara da cewa wahalar shiga yankin cikin gaggawa ta kawo tsaiko wajen tantance ainihin asarar da aka yi, amma binciken bayan harin ya tabbatar da cewa an kashe wasu daga cikin ’yan ta’addan da aka kai wa hari.
A yanzu haka dai rundunar sojin Nijeriya na ƙara amfani da jiragen yaƙi marasa matuƙa wajen kai hare-hare kan maboyar ’yanbindiga a yankunan dazuzzuka da sauran wuraren da suke fakewa a Arewa maso Yammacin ƙasar.
