Connect with us

Politics

Murmushin Samun Nasara 

Published

on

images 49 (1)

Daga Abba Anwar 

 

Advertisement

Ni dai tuntuni na san irin kyakkyawan wakilci nagari da kuma ayyukan alherin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Maigirma Sanata Barau I Jibrin, CFR, PhD, yake yi, ina da tabbacin cewa jiga-jigan siyasa na Kano ta Arewa, ba za su taba bari abin ya kwaranye a banza ba.

Ita fa adawa ko samun sabani a siyasa ba haram ba ne, a tsarin dimokuraɗiyya. Kuma an fi ganin irin wannan a wuraren da a ke da dandazon jagorori, kuma masu kishin al’ummar su. Dan kowannensu ya na da irin nasa karfin da tasiri a wajen mutanen sa.

Advertisement

KANO: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2 A Gwarzo ‎

Misali yanzu a Kano ta Arewa, akwai shi kansa Sanata Barau din, akwai tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, CON, akwai Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, akwai tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Abdullahi T. Gwarzo, sannan akwai dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Bichi, kuma shugaban kwamitin raba arzikin kasa na majalisar, da kuma wasu jiga-jigai daga Kano ta Arewan.

Advertisement

Dukkanin jagororin nan da na ambata, kowannensu sarki ne a cikin mutanen sa. Dukkansu su na bukatar junansu, dan samun nasarar jam’iyyar a dukkan matakai, musamman a jiha.

Samun nasarar sulhu da a ka samu tsakanin Sanata Barau da kuma ATM Gwarzo, kan takarar Sanata a zabe mai zuwa na 2027, ba karamar nasara ba ce, wacce ta samu ne saboda hobbasar wadannan jiga-jigai. Shi kuma Maigirma Gwamna Kano, Abba Kabir Yusuf, ba karamin shugabanci nagari ya nuna ba wajen tsayin daka da ya yi na tabbatuwar wannan abin. Tabbas ya nuna kwarewa da hangen nesa a mulki da siyasa.

Advertisement

Haka nan bayan samun wannan daidaituwa na ji wata hira da Sanata Barau ya yi da ‘yan jarida, har na ji ya yabawa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, wato Maigirma Ibrahim Masari. Hakan ya nuna mana irin kokarin da Masarin ya yi wajen ganin an yi maganin kowace irin baraka da ka iya kawo cikas. Dan haka ya zama wajibi shi ma a yaba masa.

Ni fa a gani na, wannan abin da Masarin ya yi, ya na nuni da irin damuwa da jihar da shugaban kasa ya yi ne, wajen samun nasarar jam’iyyar APC da kuma cigaban jihar. Ban dai ga wajen da Masarin ya je ya yi irin wannan aiki ba da ya hada da mai babban mukami irin na Barau ba. Ni dai ban gani ba, ban kuma sani ba.

Advertisement

A dalilin wannan cigaban da a ka samu kuma, na san Maigirma Sanata zai kara fahimtar cewar ashe dai jama’arsa na matukar jin dadin yadda yake kawo musu ci gaba a mazabarsa ta Kano ta Arewa. Daga ciki kuwa har da wadanda a ke wa kallon abokan adawarsa, a da kafin sulhu, na siyasa.

Samun nasara da kuma Sanata Barau, kamar yan tagwaye ne. Daya ya na manne da dayan. Tabbas irin wannan tsarin namu na dimokuraɗiyya ya na bukatar jajirtattun jagorori irin sa. Ga kishin al’umma, ga sanin me mazabarsa da yankin sa na arewa ke bukata.

Advertisement

Hadewar Barau da Garo da Gwarzo waje daya, shine yake kara tabbatarwa da kowa cewar, har yanzu dai jam’iyyar APC a jihar Kano ta fi karfi da tasiri da mamaya, a Kano ta Arewa. Sama da ragowar shiyyoyin jihar. Wato Kano ta Tsakiya, wacce na fito daga ciki, da kuma Kano ta Kudu. Su jagororin Kano ta Arewa din sun fi ragowar jagororin kishin jam’iyyar da kuma neman dukkan hanyoyin samun nasarar jam’iyyar. In gaya maka dalili? Zaben 2023.

Bayan wannan sulhu da a ka samu, ni a ganina, yanzu ba wai dan ta-fadi-gasassa ba ne kawai zai koma daga baya ya na kara kulla wata wutar gaba ba, illa shaidan. Duk kankantantar mutum a jam’iyya kuwa. Kuma duk girman sa. Babban abin dadin ma kawai shine, Allah Ya hore mana tsayayyen gwamna. Mai adalci. Saboda haka duk wasu kulle – kulle za su tashi a banza ne.

Advertisement

Anwar ya rubuto daga Kano 

Juma’at, 15 ga Watan Mayu, 2026

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending