News
Saboda Tallata Manufofina Ya Sa Nake Ƙoƙarin Ƙwace Uranium Ɗin Iran – Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ƙoƙarin ƙwace sinadarin Uranium daga Iran ba komai bane face neman farin jinin siyasa da tallata manufofinsa a idon duniya, saɓanin dalilin tsaro da ake ta magana a kai.
Trump na bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a birnin Beijing na ƙasar China.
Kalaman shugaban na Amurka sun saɓawa buƙatun Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya dage cewa yaƙin da ake yi da Iran ba zai ƙare ba har sai an kwashe dukkanin sinadaran Uranium daga ƙasar.
Trump ya bayyana cewa ko da ba a kwashe sinadarin ba, zai ji daɗi a ransa idan Amurka ta samu nasarar ƙwace shi, amma babban dalilin anan shi ne nuna bajinta ta siyasa.
Trump ya ce ko da sinadarin yana binne a ƙarƙashin ƙasa bayan bama-baman da Amurka da Isra’ila suka jefa, dakarun sararin samaniya na Amurka suna sa ido a kai ta tauraron ɗan adam, kuma za su jefa makami mai linzami kan duk wanda ya kusanci wurin.
