News
“An Mayar Da Siyasa Fagen Cin Mutunci A Najeriya” — Sheikh Daurawa
Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a Nijeriya da su gyara tsarin siyasa tare da kauce wa ƙage, sharri da yaɗa ƙarya da ke ƙara haddasa rarrabuwar kai a tsakanin al’umma.
Malamin addinin ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya nuna damuwa kan yadda siyasa ta sauya daga hanyar hidima da haɗin kai zuwa fagen gaba, ƙiyayya da ɓata sunan juna.
A cewarsa, a yanzu an fi mayar da hankali wajen yaɗa jita-jita marasa tushe, ƙirƙirar labaran ƙarya da cin mutunci a kafafen sadarwa domin cimma muradun siyasa.
Sheikh Daurawa ya ce wannan yanayi na jawo rashin amincewa tsakanin shugabanni da jama’a, tare da ƙara haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan siyasa da kuma lalata tarbiyyar matasan da ke tasowa cikin harkokin siyasa.
Ya ƙara da cewa yawaitar irin waɗannan rikice-rikice na hana ƙasa samun cikakken ci gaba da zaman lafiya.
“Addini da hankali suna koyar da gaskiya da adalci tare da kiyaye mutuncin mutane. Musulunci ya haramta ƙage, gulma da cin mutunci saboda illar da suke yi ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma,” in ji shi.
Malamin ya bayyana cewa siyasa ta gari ita ce wadda ta ginu kan gaskiya da hujja maimakon zagi da cin fuska, tare da fifita kishin ƙasa da haɗin kai sama da son zuciya.
Ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su gyara harsunansu da niyyarsu, yana mai cewa idan aka guji sharri da ƙage, siyasa za ta zama hanyar samar da ci gaba da zaman lafiya maimakon fitina da gaba.
A ƙarshe, Sheikh Daurawa ya yi addu’ar Allah Ya shiryar da shugabanni da al’umma baki ɗaya.
