News
Yansanda Sun Cafke Mutane 248 Da Ake Zargi Da Laifuka A Kano
Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta sanar da kama mutane 248 da ake zargi da hannu cikin aikata laifuka daban-daban a fadin jihar, biyo bayan wani samame da jami’an tsaro suka gudanar.
Kwamishinan ’Yansandan jihar, Ibrahim Adamu-Bakori, ne ya bayyana hakan ranar Laraba yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan halin tsaro da kuma nasarorin da rundunar ta samu a jihar.
Yansanda Sun Cafke Mutane 248 Da Ake Zargi Da Laifuka A Kano
Ya ce kamen ya biyo bayan wani gagarumin aiki na tattara bayanan sirri, sa ido da kuma hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro karkashin rundunar hadaka.
A cewarsa, daga cikin wadanda aka kama akwai masu fashi da makami 18, masu garkuwa da mutane biyar, dillalan miyagun kwayoyi 32, barayin mota 12, barayin keke 11, barayin babura shida, da wasu barayi 15, yayin da aka kama mutane 149 da ake zargi da tayar da tarzoma da hana zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Kwamishinan ya kara da cewa jami’an tsaro sun samu nasarar ceto mutum uku daga hannun masu garkuwa da mutane tare da mayar da su cikin iyalansu lafiya.
Adamu-Bakori ya ce rundunar ta kuma kwato makamai daban-daban da suka hada da bindiga kirar pistol guda daya, wata bindigar pistol da ake hadawa a gida, da kuma doguwar bindiga tare da harsasai biyar.
Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da adduna 232, wukake 374, gatarai 13, almakashi 58, kwari biyu, baka 23, sanduna 37, da daruruwan kunshin abin da ake zargi tabar wiwi ne, da kuma katon hudu na kayan maye da ake zargi. Haka kuma an kwato kwayar Exol guda 291 tare da wasu kayan maye da wayoyin hannu.
“Dukkan wadanda ake zargi muna ci gaba da gudanar da bincike a kansu, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike,” in ji Kwamishinan.
Ya bayyana cewa bayan wasu rikice-rikicen da aka samu a jihar, rundunar ta kara tsaurara matakan tsaro a yankunan Panshekara, IBB Road da Hotoro domin tabbatar da zaman lafiya.
A karshe, Kwamishina Adamu-Bakori ya yaba wa shugabannin addinai, masu sarautun gargajiya da kungiyoyin matasa bisa hadin kan da suke bai wa jami’an tsaro wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sannan ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai tare da rika kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.
