News
Jami’an Yansanda Sun Kama Matashi Kan Kashe Kakansa Da Wuka
Rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi ta sanar cewa ta fara bincike kan wani matashi da ake zargin ya kashe kakansa mai shekara 70 da wuƙa a ƙauyen Sabon Kariya na Karamar Hukumar Ganjuwa .
Wani mazaunin ƙauyen, mai suna Habib mai shekaru 58 ya shaida wa ’yan sanda cewa suna zargin matashin ya caka wa kakansa mai suna Ibrahim Maisaje da wuka, bayan samun jikan da aka yi a ɗakin mamacin.
Wani Ɗan Kasuwa Ya Rasu Yayin Rikici Da Ɗansa A Abuja
Ya ƙara da cewa jami’an ‘yan sanda sun garzaya wurin da abin ya faru nan take, inda suka ɗauki gawar suka kai ta Asibitin Gwamnati da ke Kafin Madaki, inda likita ya tabbatar da rasuwar dattijon.
Advertisements
