News
Pantami Ya Zama Dan Karar Gwamnan Gombe A PDP
Tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya dan takarar Jam’iyyar PDP na Gwamnan Jihar Gombe a zaben 2027.
Pantami ya zama dan takarar PDP ne bayan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar, bayan ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC.
Kotu Ta Kori Shari’ar Neman Hana Jonathan Takara
Tsohon ministan ya zama dan takara ne bayan ya samu amincewar mambobin PDP a yayin zaben fitar da gwari a ranar Talata.
Mambobin jam’iyyar sun amince da shi ne ta hanyar daga murya, bayan ya kasance mai neman takarar kujerar shi kadai a PDP.
Shugaban kwamitin zaben fid-da-gwanin, Honorabul Gregory Yenlong ne ya sanar da nasarar Pantami.
Da yake jawabi bayan an bayyana shi a matsayin dan takara, Pantami ya ce, ya fito neman kujerar ce domin hidimta wa jama’ar Jihar Gombe.
Ya kuma yi alkwarin adalci da gaskiya idan ya zama gwamnan jihar.
