News
KATSINA: Ana Fargabar Mutuwar Mutane 16 Bayan Harin ‘Yan Bindiga A Dutsinma
’Yan ta’adda sun bindige wasu mutum 16, a yayin wasu da dama suka ɓace a ƙauyen Kuliya da ke daura da Bagagadi a Ƙaramar Hukumar Dutsinma ta Jihar Katsina.
’Yan ta’addan sun fara wa ƙauyen ne jim kaɗan bayan an idar da Sallar Juma’a, a yayin da jama’a suka ci gaba da harkokinsu da shaulgulan Sallah.
Gwamnoni Na Duba Yiwuwar Karin Mafi Karancin Albashi Zuwa Naira 100,000 — Gwamnan Kwara
Majiyarmu ta bayyana cewa da farko ’yan bindiga biyu a bisa babura ne suka fara shigowa ƙauyen, inda mutane suka fara guje-guje, amma suka umarce su da su tsaya.
Majiyar ta ce, daga baya ’yan bindigar suka je gidan wani bakanike, kwatsam kuma sai suka fara buɗe wa mutane wuta.
“Bayan mun idar da sallar Juma’a, muna zaune tare da wasu, har na kira wani yaro mai sayar da kunu na sayi kwano guda a wurinsa, a daidai lokacin ne ’yan bindigar suka iso.
“Na ga mutum biyu daga cikinsu a kan babur. Nan take mutane suka fara gudu, sai suka ce kada mu gudu. Amma kwatsam suka fara harbe-harbe.
“Ni da yaron muka ruga cikin wani gida muka ɓoye. Muna ɓoye, muna jin ihun mutane da ƙarar harbe-harbe a ko’ina. Bayan wasu mintuna, harbe-harben suka lafa.
“Da muka fito, sai muka tarar da gawarwakin kusan mutum 16 kwance, ciki har da wasu kawunnaina da ’yan uwana,” in ji shi.
Majiyar ta ce, bayan harin, mutane kimanin 400 sun fice daga yankin domin neman mafaka a Bagagadi, wasu sun koma ƙauyen Raɗɗa. Wasu da dama kuma ba a san inda suke ba, tun bayan harin.
A cewarsa, akai alamar cewa an tsinci gawar wasu daga cikin mutanen a gonaki a kusa da ƙauyen.
Wani shaida ya bayyana cewa wasu ƙarin ’yan bindiga sun shigo, suka buɗe wuta babu ƙaƙƙautawa a kan mutanen ƙauyen.
Wani mazaunin ƙauyen Bagagadi da ke maƙwabtaka da Kiliya ya shaida wa wakilinmu cewa sama da mutum 30 da suka tsere daga harin da aka kai ƙauyen Kiliya, galibinsu mata da yara, suna samun mafaka a gidansa a halin yanzu.
Haka kuma, bayanai sun nuna cewa harin na iya kasancewa ramuwar gayya ce. Majiyoyi sun bayyana cewa wasu mazauna yankin sun kashe wasu da ake zargin ’yan bindiga biyu kwanaki kaɗan kafin harin.
“Daga yadda aka kai wannan hari, alamu sun nuna cewa ramuwar gayya ce, domin kwanaki kaɗan da suka gabata an kashe ’yan bindiga biyu na wani gungun fitacciyar ƙungiyar ’yan bindiga. Wataƙila hakan ne ya sa suka kai wannan hari,” in ji wata majiya.
Sai dai da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce har zuwa lokacin da aka yi magana da shi, rundunar ba ta samu rahoton harin ba. Ya kuma yi alƙawarin cewa zai bayar da ƙarin bayani da zarar rundunar ta samu rahoto.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, kakakin rundunar bai sake tuntuɓar wakilinmu ba domin ƙarin bayani.
