Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Sace Dalibai 7 A Zamfara.

Published

on

images (8)

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da dalibai shida na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) da ke Kaura Namoda a Jihar Zamfara, bayan sun kai hari gidan da daliban ke zaune a wajen harabar makarantar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wani gida da ke gefen unguwar Low-Cost a garin Kaura Namoda, inda maharan suka kutsa cikin gidan tare da yin awon gaba da daliban.

Advertisement

Shugaban Karamar Hukumar Kaura Namoda, Alhaji Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da kubutar da daliban cikin koshin lafiya.

“Lamarin ya faru, kuma jami’an tsaro suna ci gaba da gudanar da aiki domin ceto daliban da aka sace tare da mayar da su ga iyalansu lafiya,” in ji shi.

Advertisement

Wani dalibi a makarantar, Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ya samu damar kubuta daga hannun maharan, lamarin da ya rage adadin wadanda ke tsare zuwa shida, wadanda suka hada da maza uku da mata uku.

Ita ma Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce jami’an rundunar tare da dakarun Operation Fansan Yamma sun fara wani samame na musamman domin ceto daliban.

Advertisement

Ya ce binciken farko ya nuna cewa maharan sun samu damar shiga gidan ne bayan daya daga cikin daliban ya fita da dare, inda aka yi zargin ya bar kofar gidan a bude.

DSP Yazid ya kara da cewa duk da aukuwar lamarin, harabar makarantar na nan cikin tsaro saboda kasancewar jami’an tsaro da aka jibge a yankin.

Advertisement

Ya tabbatar da cewa jami’an rundunar na ci gaba da kokarin gano maboyar maharan da kuma ceto daliban cikin gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending