News
DAMINAR 2026: Yankuna 148 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa A Jigawa – NEMA
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana cewa yankuna 148 da ke cikin kananan hukumomi 17 na Jihar Jigawa na cikin hadarin fuskantar mummunar ambaliyar ruwa a lokacin daminar shekarar 2026.
Hukumar ta yi wannan gargadi ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan shirin tunkarar bala’o’i da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar, inda ta bukaci jama’a da hukumomi su dauki matakan kariya tun kafin ambaliyar ta afku.
Yan Ta’adda Sun Sace Jariri Dan Wata 7 A Borno
Babbar Daraktar NEMA, Hajiya Zubaida Umar, wadda Daraktan shiyyar Arewa maso Yamma, Aliyu Shehu, ya wakilta, ta ce yankunan da ke bakin koguna da hanyoyin ruwa su ne suka fi fuskantar barazanar ambaliya a bana.
Ta bayyana cewa taron, mai taken “Karfafa Gudanar da Hadarin Bala’o’i Domin Gina Najeriya Mai Juriya,” na daga cikin kokarin hukumar na rage illolin ambaliya da sauran bala’o’in da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a fadin kasar nan.
NEMA ta yi kira ga mazauna yankunan da ke fama da ambaliya a kowace shekara da su kaurace wa wuraren da ke cikin hadari, su guji zubar da shara a magudanan ruwa tare da bin umarnin hukumomi da hasashen yanayi da ake fitarwa lokaci zuwa lokaci.
Hukumar ta jaddada cewa ambaliya na daga cikin manyan bala’o’in da ke haddasa asarar rayuka, lalata gidaje, gonaki da muhimman kayayyakin more rayuwa a Najeriya.
A nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Alhaji Hannafi Yakubu, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta dauki matakan da suka dace domin tunkarar duk wata ambaliya da ka iya afkuwa.
Ya ce gwamnatin jihar ta samar da kwale-kwalen ceton gaggawa guda 20 domin saukaka ayyukan ceto da kwashe jama’a daga yankunan da ambaliya za ta iya shafa.
Hannafi ya kara da cewa an tanadi kayan agaji na abinci da wadanda ba na abinci ba domin tallafa wa mutanen da bala’in ambaliya ka iya raba da muhallansu.
Har ila yau, Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa tana ci gaba da share magudanan ruwa da gudanar da ayyukan tsaftar muhalli domin inganta hanyoyin kwararar ruwa da rage yiwuwar ambaliya a cikin birane da karkara.
Masu ruwa da tsakin da suka halarci taron sun bukaci a kara karfafa tsarin gargadin wuri, wayar da kan jama’a da kuma hada kai tsakanin hukumomi domin rage illolin ambaliya.
