News
Gwamnatin Tarrayya Ta Ware Naira Bilyan 10 Domin Dakike Barazanar Cutar Ebola
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin don lura da kuma sa ido kan barazanar ballewar annobar Ebola a kasar.
Bayanin hakan na kunshe cikin sanarwar da maitaimakawa shugaban kasa kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar a yammacin ranar Talata.
Onanuga ya ce shugaba Tinubu ya ba da umarnin fitar da Naira Miliyan Dubu goma don fara tunkarar matsalar.
A cewarsa kudin zai taimaka wajen karfafa shirye-shirye na kar ta kwana.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, ne zai jagoranci kwamitin, sai kuma mambobi daga maaikatar lafiya da kuma wakilan jihohi.
Advertisements
