News
Ana Zargin ‘Yan Mata Na Sayar Da ‘Kwayayan Haihuwarsu’ Domin Sayan Manyan Wayoyi A Filato
Hukumar samar da daidaito da kare hakkokin mata ta jihar Plateau (PLASGEOC) ta bayyana damuwarta kan yadda wasu ƴan mata, ciki har da daliban manyan makarantu, ke sayar da kwayoyin haihuwarsu (ova) domin samun kudi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito shugabar sashen yada labarai ta hukumar, Nene Dung, ce ta bayyana hakan yayin wata tattaunawa a shirin Hausa na “Mutattauna” da ake gabatarwa a gidan rediyon Unity FM da ke Jos.
Kotu Ta Umarci Hukumar INEC Ta Yi Wa Jam’iyyar Access Party Rajista
A cewarta, binciken da hukumar ta gudanar ya gano wani asibitin haihuwa da ke karbar kwayoyin haihuwa daga mata, inda ta bayyana lamarin a matsayin cin zarafi da kuma wani nau’i na cin zarafin mata da ya danganci jinsi.
Dung ta ce masu neman haihuwa na biyan makudan kudade a irin wadannan cibiyoyi, yayin da wasu ’yan mata ke sayar da kwayoyin haihuwarsu domin sayen wayoyi masu tsada ko kuma daukar nauyin kansu.
Ta bayyana cewa wadanda suka sayar da kwayoyin haihuwar kan karbi tsakanin naira 120,000 zuwa 150,000 bayan an cire musu kwayoyin.
Hukumar ta ce ta fara wayar da kai a makarantu da al’ummomi domin fadakar da mata kan illolin wannan dabi’a tare da kare su daga duk wani nau’in cin zarafi.
A cewar Dung, hukumar na shirin ganawa da shugaban Jami’ar Jos kan batun, kuma tuni ta tattauna da shugabannin Kwalejin Fasaha ta Barkin Ladi, Kwalejin Ilimi ta Gindiri da kuma Jami’ar Ilimi ta Pankshin.
-
News7 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
