News
Gwarzo Ya Kalubalanci Gwamnatin Kano Kan Zargin Karɓar Kuɗaɗen Kananan Hukumomi
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kalubalanci Gwamnatin Jihar Kano da ta fito da sahihan hujjoji kan zargin da ake yi masa na karɓar kuɗaɗen kananan hukumomi ta hannun ɗansa, Mujahid Aminu Abdussalam.
Takaddamar ta samo asali ne bayan mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi zargin cewa wasu kuɗaɗen kananan hukumomi sun riƙa shiga hannun tsohon mataimakin gwamnan ta hanyar ɗansa.
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Mutum Da Wayoyin Sata Guda 36
Sai dai a wata sanarwa da kakakinsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar ranar Alhamis, Gwarzo ya musanta zargin gaba ɗaya, yana mai cewa babu wata hujja da ke tabbatar da irin wannan ikirari.
Ya bayyana zargin a matsayin wani yunkuri na bata masa suna a idon jama’a, tare da neman masu zargin su gabatar da cikakkun hujjoji idan har suna da tabbacin abin da suke faɗa.
A cewar sanarwar, Gwarzo ya ce tun lokacin da ya fara rike mukaman gwamnati, ya kasance mai bin doka, gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da harkokin jama’a.
Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa gaskiya za ta bayyana a ƙarshe, yana mai kira ga al’ummar jihar da su yi taka-tsantsan wajen yarda da zarge-zargen da ba a gabatar wa jama’a hujjoji a kansu ba.
Lamarin na ci gaba da jan hankali a Kano, yayin da jama’a ke jiran karin bayanai daga bangarorin da abin ya shafa domin fayyace gaskiyar zarge-zargen da ake musayarwa.
