News
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Dukkan Kamfanonin Siminti Da Su Rage Farashi
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bukaci masana’antun siminti a Najeriya da su rage farashin kayayyakinsu, yana mai gargadin cewa tsadar siminti na kawo cikas ga ayyukan gine-ginen more rayuwa tare da ƙara wa gwamnati nauyin gudanar da kwangiloli.
Umahi ya bayyana haka ne a wani taron ƙaddamar da sabon sunan kamfanin Lafarge, wanda yanzu ya koma HBM, kuma ya shiga ƙarƙashin rukunin kamfanonin HUAXIN Group, da aka gudanar a Legas ranar Lahadi.
Rashin Halartar Kotu Ya Jawo Tsare Sowore A Gidan Gyaran Hali
Ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta fara zama da masana’antun siminti daga ranar 1 ga watan Yuli domin tattauna hanyoyin da za a rage farashin siminti, wanda ya ce ya zama babban ƙalubale ga masu aiwatar da ayyukan gine-gine a ƙasar.
Ya bayyana cewa raguwar farashin siminti za ta taimaka wajen rage kuɗin ayyukan gwamnati da kuma sauƙaƙa wa al’umma gina gidaje da sauran muhimman gine-gine.
Umahi ya kuma yi kira ga kamfanin HBM da sauran masana’antun siminti su ƙara yawan samar da kayayyaki domin biyan buƙatun da ke ƙaruwa sakamakon manyan ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa.
Har ila yau, ya yaba wa kamfanin bisa ci gaba da zuba jari a Najeriya, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari domin bunƙasa harkokin masana’antu da ci gaban tattalin arziki.
