Connect with us

News

Kudirin Kafa Yansandan Jahohi Na Iya Lashe Sama Da Naira Biliyan 800 ‎ —Masana

Published

on

Advertisements
ads

Masana kan harkokin tsaro da tattalin arziki sun bayyana damuwa kan irin dimbin kudaden da za a kashe idan aka fara aiwatar da kudirin kafa rundunar ’yan sandan jihohi a Najeriya, duk da cewa mutane da dama na maraba da shirin domin inganta tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa aiwatar da tsarin na iya cin tsakanin Naira biliyan 589 zuwa Naira biliyan 813 cikin shekaru biyar, domin samar da cibiyoyi, horas da jami’ai, sayen kayan aiki da gina tsarin gudanar da rundunar a jihohin kasar nan.

Ɓangarorin Da Amurka Da Iran Suka Gaza Cim Ma Matsaya Cikin Yarjejeniya

‎Masana sun yi gargadin cewa, duk da muhimmancin samar da ’yan sandan jihohi wajen magance matsalolin tsaro, akwai bukatar gwamnati ta samar da ingantaccen tsarin samar da kudade domin kauce wa nauyi ga jihohin da ke fama da karancin kudaden shiga.

‎Rahoton kwamitin da ya yi nazari kan shirin ya nuna cewa za a bukaci a gina hukumomin kula da ’yan sandan jihohi, cibiyoyin horaswa, cibiyoyin binciken kimiyyar laifuka, da kuma tsarin fasahar sadarwa kafin rundunar ta fara aiki yadda ya kamata.

‎A cewar masu sharhi, wasu jihohi masu karancin karfin tattalin arziki na iya fuskantar matsalar daukar nauyin biyan albashi da gudanar da ayyukan rundunar, lamarin da zai iya zama babban kalubale idan ba a samar da ingantaccen tsarin tallafi ba.

Advertisement

‎Sai dai masu goyon bayan kudirin na ganin kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen kusantar jami’an tsaro da al’umma, inganta tattara bayanan sirri da kuma saurin kai dauki lokacin da ake fuskantar barazanar tsaro.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending