Connect with us

Opinion

YAƘI DA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN ƘWAYOYI A KANO: Gagarumin Aiki Ne Ke Gaban Kwamitin Muhuyi Rimingado

Published

on

images (11)
Advertisements
ads

Daga Abbas Ibrahim

Kafa Kwamitin Musamman Kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Fataucin Su da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi, na ɗaya daga cikin matakan da suka zo a daidai lokacin da jihar ke ƙara fuskantar barazanar  shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi ke yi ga tsaro, lafiya da makomar matasa.

A tsawon shekaru, Kano na ci gaba da fama da matsalar shan miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa. Duk da irin muhimmancin da jihar ke da shi a matsayin cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya, hakan ya kuma sa ta kasance cikin wuraren da masu safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙoƙarin amfani da su wajen gudanar da haramtattun ayyukansu.

Gwamnatin Tarrayya Za Ta Sake Nazari Kan  Mafi Ƙarancin Albashi Na N70,000

Abubuwan da suka fito fili a Taron Ƙasa Kan Tsaro da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) tare da haɗin gwiwar Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) suka shirya a Abuja a ranar 18 zuwa 19 ga Yuni, sun sake jaddada cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi ya zama wajibi.

A yayin taron, wakilin shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Janar Mohammed Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana cewa shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron ƙasa, lafiyar jama’a da ci gaban matasa.

Advertisement

Wannan ne ya sa matakin gwamnatin Kano na kafa kwamitin ya samu karɓuwa daga masu ruwa da tsaki. Haka kuma, naɗin Barrista Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin shugaban kwamitin, tare da haɗa jami’an tsaro, hukumomin gwamnati da fitattun masu aikin sa-kai, ya ƙara ɗaga fatan al’umma cewa za a gudanar da aikin cikin gaskiya da ƙwarewa.

Sai dai, kafa kwamitin ba shi ne babban ƙalubale ba. Babban abin dubawa shi ne ko zai iya samar da sakamakon da al’umma ke jira.

A baya ma an kafa kwamitoci da shirye-shiryen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Kano, amma duk da wasu nasarorin da aka samu, matsalar ta ci gaba da ƙaruwa. Wannan na nuna cewa yaƙin na buƙatar sabbin dabaru da haɗin kan gwamnati, hukumomin tsaro da al’umma baki ɗaya.

Shan miyagun ƙwayoyi ba matsalar laifi kaɗai ba ce. Matsala ce da ke shafar tattalin arziki, lafiya, zaman lafiyar iyali da tsaron al’umma. Haka kuma, masana harkokin tsaro sun yi imanin cewa yawancin laifukan daba, fashi da makami, rikice-rikicen cikin gida da sauran miyagun ayyuka na da alaƙa da shaye-shaye.

Saboda haka, ana sa ran kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin gaskiya, adalci da rashin nuna son kai. Haka kuma, dole ne ya kauce wa duk wani tasiri daga masu faɗa a ji ko masu neman kare masu aikata laifuka.

Wani muhimmin ginshiƙi na nasarar wannan yaƙi shi ne tattara sahihan bayanan sirri. Ya zama wajibi kwamitin ya ƙarfafa haɗin gwiwa da shugabannin gargajiya, malamai, ƙungiyoyin matasa da hukumomin tsaro domin gano da kuma rushe hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

Haka kuma, sabuwar rundunar Kano Neighbourhood Watch Corps, wadda aka tura a sassa daban-daban na jihar, na iya taka muhimmiyar rawa wajen samar da bayanan sirri daga matakin al’umma.

Idan kuma aka samu nasarar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeriya, hakan zai ƙara ƙarfafa ikon jihohi wajen yaƙar manyan laifuka da suka haɗa da fataucin miyagun ƙwayoyi.

A ƙarshe, nasarar kwamitin ba za a auna ta da yawan tarurrukan da ya gudanar ko sanarwar da ya fitar ba. Za a auna ta ne da irin raguwar shaye-shaye, lalata cibiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi, gyaran rayuwar matasa da suka kamu da wannan annoba, da kuma inganta tsaro da zaman lafiya a Kano.

Al’ummar Kano na sa ido tare da ɗora babban fata a kan wannan kwamitin. Matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka ya nuna an fara tafiya, amma yanzu nauyi ya rataya a wuyan shugabannin kwamitin ƙarƙashin jagorancin Barrista Muhuyi Magaji Rimingado su tabbatar da cewa wannan yunƙuri zai haifar da sakamako mai ɗorewa.

Yaƙi da miyagun ƙwayoyi ba kawai yaƙi da masu laifi ba ne, yaƙi ne domin kare makomar matasan Kano, tabbatar da zaman lafiyar al’umma da kuma kare tsaron jihar baki ɗaya.

 

Advertisement

Comrade Abbas Ibrahim, a crime and Judicial Reporter writes from Kano and can be reached at abbasibrahim664@gmail.com

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending