News
An Gano Macizai Sama Da 300 A Gidan Wani Dan Kasar China

Wani abin mamaki ya faru a ƙasar China bayan jami’an tsaro sun gano wani ɗaki a cikin gidan wani mutum cike da macizai har guda 309, waɗanda aka kiyasta darajarsu ta haura dala miliyan huɗu.
Rahotanni sun bayyana cewa binciken ya kai jami’an tsaron zuwa gidan ne bayan an lura da yawan amfani da wutar lantarki fiye da kima, wanda daga bisani ya tona asirin wata haramtacciyar cibiyar kiwon macizai a cikin gidan.
Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Soke Hukuncin Rijistar Jam’iyyar NDC
Mutumin, mai suna Gua (Guo), ya mayar da yawancin ɗakunan gidansa wuraren kiwon macizai, inda aka tarar da su cikin akwatunan roba a jere. Binciken ya kuma gano cewa ana zargin an yi safarar wasu daga cikin macizan tare da sayar da su ba tare da izinin hukuma ba.
Kotun da ke birnin Taizhou na lardin Zhejiang ta yanke wa Gua hukuncin zaman gidan yari tare da wasu abokan hulɗarsa, bisa laifin kiwo da fataucin dabbobin da ke ƙarƙashin kariyar doka a China. Sai dai kotun ba ta bayyana tsawon wa’adin hukuncin da aka yanke musu ba.
Bayan kama mutumin, ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi sun kwashe macizan zuwa gidan adana namun jeji da ke yankin Taizhou, domin kula da su cikin yanayi mai aminci. Hukumomi sun bayyana cewa jimillar darajar macizan da aka gano ta kai sama da dala miliyan huɗu, lamarin da ya sanya wannan shari’a cikin manyan batutuwan da suka shafi fataucin namun daji a ƙasar China.
