News
An Kone Mutane 18 Da Ransu Sakamakon Rikici Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Niger
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutane 18 sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Rafi ta jihar.
Al’ummomin da rikicin ya shafa sun haɗa da Anguwan-Baago, Kuwan-Kasa, Mararraban-Gwadaro da Tashan-Bako.
Dakarun Soji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 1,500 A Cikin Watanni Shida
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa mutane 15 daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu an ƙone su da ransu a cikin ɗakunansu a ƙauyen Anguwan-Baago.
A cewarsa, rikicin ya fara ne tun ranar 29 ga Yuni, kafin ya ƙara ƙamari a ranar 1 ga Yuli bayan hare-haren ramuwar gayya da suka biyo baya.
Ya bayyana cewa wasu da ake zargin ɗauke da makamai sun kashe wani matashi mai shekaru 25 mai suna Ibrahim Musa a ƙauyen Godoro a ranar 29 ga Yuni.
Bayan wannan lamari, wasu mambobin ƙungiyar tsaro ta sa-kai sun toshe hanya, inda suka kashe wani mutum mai shekaru 28 mai suna Bashir Mazi, lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin.
SP Abiodun ya ce binciken farko ya nuna rikicin na da alaƙa da tsohuwar takaddamar filaye tsakanin manoma da makiyaya, wanda daga bisani ya bazu zuwa wasu ƙauyukan da ke yankin.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙaramar hukuma ta kafa kwamitin sulhu da ke aiki tare da hukumomin tsaro domin shawo kan rikicin da kuma dawo da zaman lafiya.
Hakazalika, ya ce an tura jami’an tsaro na haɗin gwiwa da suka haɗa da ’yan sanda da sojoji zuwa yankunan da abin ya shafa domin dakile ƙarin tashin hankali da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai wasu mazauna yankin sun yi sabani da alkaluman da rundunar ’yan sanda ta fitar, inda suka yi iƙirarin cewa adadin waɗanda suka mutu ya fi 18, suna masu cewa har zuwa ranar Alhamis ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a wasu sassan yankin.
