News
Andy Burnham Zai Karbi Ragamar Mulkin Birtaniya A Matsayin Sabon Firaminista
Ana sa ran Andy Burnham zai karbi ragamar mulkin Birtaniya a yau Litinin, inda zai zama sabon Firaministan kasar bayan murabus din Keir Starmer.
Burnham mai shekaru 56 zai zama mutum na shida da ya jagoranci gwamnatin Birtaniya tun daga shekarar 2016, a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubale na tattalin arziki da siyasa.
Rahoton Samun Masu Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai a Hukumomin Tsaro Ya Jawo Cece-kuce
Keir Starmer ya yi murabus ne shekaru biyu bayan ya jagoranci Jam’iyyar Labour zuwa nasarar da ta kawo karshen mulkin Jam’iyyar Conservative na tsawon shekaru 14.
Bayan Sarkin Birtaniya, Charles na Uku, ya bukace shi da ya kafa sabuwar gwamnati, Burnham zai gabatar da jawabinsa na farko a gaban ofishin Firaminista da ke lamba 10 Downing Street bayan mika mulki.
A wata hira da ya yi da jaridar The Times, Burnham ya ce babban burinsa shi ne kawo sauyi a tafiyar da gwamnati da kuma rage rikice-rikicen siyasar da suka addabi kasar.
Ya ce, “Abin da muka kasance muna yi bai samar da sakamakon da ake bukata ba. Ina son gwada wata sabuwar hanyar shugabanci.”
Tawagar Burnham ta bayyana cewa a jawabinsa na farko zai yi alkawarin dawo da amincewar jama’a ga gwamnati, rage tsadar rayuwa da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.
Ana kuma sa ran zai sanar da sunayen sabbin ministocinsa, ciki har da wanda zai maye gurbin Rachel Reeves a matsayin Ministan Kudi.
Kafin wannan nadi, Burnham ya kasance Magajin Garin Greater Manchester, inda ya shahara da lakabin “Sarkin Arewa” saboda irin tasirin da yake da shi a siyasar arewacin Ingila.
Jam’iyyar Labour ta zabe shi a matsayin sabon shugabanta bayan murabus din Starmer, tana mai bayyana cewa tana da yakinin Burnham zai jagoranci jam’iyyar wajen fuskantar kalubalen siyasar da ke gabanta, musamman daga Jam’iyyar Reform UK.
