Connect with us

News

‎Gwamnati Ta Na Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro ‎ ‎—Tsohon sufetan ƴan sandan Najeriya Mike Okiro

Published

on

Mike Okiro

Tsohon sufetan ƴan sandan Najeriya Mike Okiro ya zargi gwamnatin tarayya da raunana rundunar ƴan sanda ta hanyar gaza samar mata da isassun makamai da kayan aikin tsaro lamarin da ya ce na ƙara ta’azzara matsalar rashin tsaro a ƙasar.

‎Da yake jawabi a taron tattaunawa kan tsaro ta ƙasa da a ka gudanar a Abuja, Okiro ya bayyana cewa rundunar ƴan sanda ita ce ke kan gaba wajen kula da tsaron cikin gida, amma rashin makamai, motocin sulke, na’urorin sadarwa da sauran kayan aiki ya rage mata ƙarfin yaƙi da masu aikata laifuka.

INEC Ta Ce Ba Za Ta Ƙara Wa’adin Rajistar Masu Zaɓe Ba

‎Ya kuma ce rashin ɗaukar sabbin jami’ai tsawon shekaru ya haifar da ƙarancin ma’aikata, inda ya bayyana cewa kusan jami’ai 59,730 sun bar aiki ta hanyar ritaya, rasuwa da sauran dalilai ba tare da an maye gurbinsu ba.

Haka kuma, tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor mai ritaya, ya nuna damuwa kan yadda a ke kashe kuɗaɗen tsaro, ya na mai cewa fiye da kashi uku cikin huɗu na kasafin kuɗin tsaro na tafiya ne wajen biyan albashin ma’aikata, yayin da kuɗaɗen sayen kayan aikin soja da sabunta su ke da ƙaranci, lamarin da ya ce na buƙatar sake duba tsarin kashe kuɗin tsaro a ƙasar.

 

Advertisement

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending