News
Babu Hidimar Ƙasa Ga Wanda NERD Ba Ta Tantance Ba – NYSC
Hukumar kula da Harkokin Ɗalibai Masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), ta gargaɗi masu shirin fara hidima kan cewa ba za a ba su damar farawa ba har sai sun samu tantancewa daga Cibiyar Rajistar Tattara Bayanai ta Laturoni ta Ƙasa (NERD).
Rahotanni sun bayyana cewa, gargaɗin na zuwa ne yayin da hukumar take cigaba da shirin karɓar tawagar ɗalibai na sabon rukuni yayin da take kuma ɗaukar matakan tabbatar da tsaronsu yayin tafiye-tafiye zuwa sansanoninsu.
Ƴansanda Sun Cafke Mutane Takwas Kan Rikicin Kasuwar Gujungu Dake Jigawa
A wata sanarwa da ta wallafa ta kafar X a ranar Litinin, NYSC ta sanar da cewa daga yanzu tantancewar NERD wajibi ne ga dukkan ɗaliban da manyan makarantu suka tura mata da nufin fara hidimar ƙasa.
Hukumar ta kuma yi kira ga ɗaliban da su yi ƙoƙarin kammala dukkan wani abin da ya shafi tantancewar akan lokaci don kauce wa dukkan wani jinkiri da ka iya samun su a yayin da suke neman fara hidima, tana mai cewa rashin hakan ka iya haifar da tsaiko a gare su.
Duk da cewa NYSC ba ta bayar da wani ƙarin bayani ba akan hanyoyin tantancewar ba, umarnin ya nuna cewa za a fuskanci tantancewa mai tsauri a yayin shirye-shiryen fara hidima na ‘yan rukuni na gaba.
Hakan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i biyu da NYSC ta sanar da karɓar wani rukunin na ‘yan hidimar ƙasa na B na 2026, tana mai kira ga makarantu da ɗaliban da suka kammala karatu da aka tantance su da su tabbatar da cika dukkan wani sharaɗi da ake buƙata domin shirin na gaba.
