Connect with us

News

Kano: Gini Ya Rufta Kan Mutane 16 Ciki Har Da Yara Shida

Published

on

Akalla mutane 16 ne gini ya rufta a kansu a yankin Dan Dishe, Kwanar Yashi, da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano.

Rahotanni sun ce jami’an ceto sun samu nasarar fitar da mutane 13 daga cikin ginin da ransu, ciki har da yara shida.

Sarkin Daura Ya Bukaci Sabon Sarkin Takutahar Ƙasar Hausa, Sheikh Abdulkadir Jiyali, Ya Yi Duk Mai Yiwuwa Domin Ci Gaban Najeriya

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ginin ya rufta da misalin ƙarfe 4:32 na asubahin ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce jami’an ceto sun garzaya wurin bayan samun kiran neman agaji.

Bayan isarsu wurin, jami’an sun gano cewa wani gini mai girman kusan ƙafa 20 da 30 ya rufta, lamarin da ya rutsa da mutane 16.

Advertisement

Hukumar ta ce an yi nasarar ceto mutane 13 da ransu, ciki har da yara shida, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin ruftawar ginin.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ko akwai wasu mutane da suka rasa rayukansu ko suka samu raunuka sakamakon lamarin ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending