Connect with us

News

Wani Fasto Ya Sassara Matarshi Da Adda Har Lahira  Ya Yin Da Ya Kwanta Tirela Ta Bi Ta Kan Shi

Published

on

Wani fasto na Cocin Celestial Church of Christ (CCC), Bidemi Odukoya, ya kashe matarsa a lokacin wata rigimar cikin gida, kafin daga bisani ya mutu bayan da ya shiga gaban wata tirela da ke tafiya a kan titin Lagos- xuwa Abeokuta Expressway a Jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na dare a ranar 31 ga Agusta, a unguwar Ogooluwa da ke Akiode Ibogun, Ƙaramar Hukumar Ifo. Rahotanni sun ce Odukoya, wanda ke jagorantar Iri Orun Parish na cocin, ya farmaki matarsa da adda da kujerar katako.

 

An ce rikicin ya samo asali ne daga zarge-zargen cin amana tsakanin ma’auratan. Bayan harin, faston ya tsere daga yankin zuwa Ifo, inda daga bisani aka ce ya shiga gaban wata babbar mota a Coker Junction, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

 

Ma’auratan sun bar ’ya’ya maza uku. An kuma binne su a kusa da gidansu bayan faruwar lamarin.

Advertisement

 

Shugaban al’ummar Akiode Ibogun, Chief Taiwo Akiode, ya ce mutuwar ma’auratan ta girgiza mazauna yankin, kasancewar sun shafe kusan shekaru tara zuwa 10 suna zaune a yankin kuma ba a san su da yawan samun rikici ba.

 

Sai dai ’yan sanda sun ce suna gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru. Mataimakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, ASP Opeyemi Oluborode, ya ce an tura fayil ɗin lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da bincike.

 

PUNCH

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending