News
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar Accord Party (AP), Ambasada Mukhtar Gashash, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wani mai sharhi kan al’amuran siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu.
An kashe Dan Shagamu a gidansa da ke unguwar Gaida, a Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin jimami da fargaba.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane Biyu Kan Zargin Hallaka Ibrahim Khalil Danshagamu A Kano
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Gashash ya bayyana kisan a matsayin “mummunan aikin ta’addanci” da ya kamata duk masu son zaman lafiya su yi tir da shi.
Ya ce bai kamata a kashe mutum saboda bayyana ra’ayinsa ba, yana mai jaddada cewa ya kamata a mutunta ra’ayoyin mutane, matuƙar ba su saɓa wa doka ba.
Gashash ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya faru, tare da kamo waɗanda ake zargi da hannu a kisan da gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar Kano da kada su ɗauki doka a hannunsu ko neman ɗaukar fansa, sai dai su bai wa hukumomin tsaro duk wani bayani da zai taimaka wajen gano waɗanda ke da hannu a kisan.
Ya ce tabbatar da adalci da tsaro ga kowa, musamman masu amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana ra’ayoyinsu, na da matuƙar muhimmanci wajen samar da zaman lafiya a jihar.
