News
Jihar Kano Ta Samu Tikitin Buga Gasar Wasanni Ta National Sports Festival 2026
Jihar Kano ta samu tikitin shiga gasar National Sports Festival 2026 a dukkan wasannin da ta fafata a gasar share fage ta shiyyar Arewa maso Yamma, wato North West Zonal Elimination, da ake gudanarwa domin tantance kungiyoyin da za su wakilci shiyyar a gasar ƙasa.
Gasar 23rd National Sports Festival 2026 za a gudanar da ita a Jihar Enugu, yayin da tawagar Kano ta nuna bajinta a wasannin da aka fafata a ranar Talata, 15 ga Satumba, 2026.
Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci Da Rashawa Na Jihar Kano Ya Yi Murabus
A wasan ƙwallon kwando na mata, tawagar Kano ta doke Zamfara da maki 47–37, lamarin da ya tabbatar mata da gurbin shiga gasar ƙasa.
A ɓangaren ƙwallon ƙafa na maza kuwa, Kano ta fara gasar da nasara a kan Sokoto da ci 2–1, kafin daga bisani ta sha kashi a hannun Kaduna da ci 1–0. Duk da rashin nasarar, Kano ta samu damar tsallakewa zuwa gasar ƙasa sakamakon sakamakon da ta samu a wasannin share fagen.
Haka kuma, tawagar Kano ta Conventional Volleyball ta samu nasara kan Sokoto da ci 2–0, yayin da jihar ta kuma samu tikitin shiga gasar a sauran wasannin da ta fafata, ciki har da ƙwallon kwando na maza da Beach Volleyball.
Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar Wasanni ta Kano, Ashiru Rabiu Gidan Tudu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 15 ga Satumba, 2026.
Shugaban Hukumar Wasanni ta Kano, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, ya bayyana farin cikinsa kan nasarar, inda ya yaba wa ’yan wasa, masu horarwa, jami’an hukumar da sauran waɗanda suka bayar da gudummawa wajen ganin an samu nasarar.
Ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa goyon baya da kulawar da gwamnatin jihar ke bai wa harkokin wasanni, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen cimma manufofin hukumar.
Mista Babangida ya kuma gode wa al’ummar Kano da masu sha’awar wasanni bisa addu’o’i da goyon bayan da suke bai wa tawagar jihar, tare da yaba wa Ƙungiyar Marubutan Wasanni ta Najeriya (SWAN), reshen Kano, bisa gudummawar da take bayarwa wajen yaɗa bayanan wasanni da ayyukan hukumar.
Ya ce yanzu hankalin hukumar ya koma kan shirye-shiryen gasar 23rd National Sports Festival 2026 da za a gudanar a Enugu, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da shirya ’yan wasan domin fafatawa a gasar ƙasa.
-
News6 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News3 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News4 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi

