News
Yau Asabar 19/09/2026 Rediyo Kano Ke Cika Shekara 80 Da Kafuwa
Radio Kano, da ke Gidan Bello Dandago, na daga cikin gidajen rediyo na farko kuma mafi dadewa a jihar Kano.
An kafa gidan rediyon ne a shekarar 1946, a matsayin reshen Radio Distribution Services (RDS) da Turawan Birtaniya suka assasa. Marigayi Alhaji Bello Dandago ne ya kasance jami’in farko na gidan rediyon.
Mun Sha Fitsarinmu Don Mu Tsira Da Ranmu — Wanda Ya Tsira Daga Mutuwar Mutane 37 A Neja
A farkon kafuwarsa, Radio Kano na isar da shirye-shirye ne ta hanyar lasifika a wuraren taruwar jama’a. Daga bisani, a shekarar 1958, aka girka na’urar watsa shirye-shirye mai karfin 1 kilowatt, wadda ta ba da damar isar da sauti a fadin birnin Kano.
Cikar Radio Kano shekaru 80 na aiki wata muhimmiyar nasara ce a tarihin yada labarai a Kano da ma Najeriya. Tsawon shekaru, gidan rediyon ya taka rawa wajen wayar da kan al’umma, musamman a lokacin gwagwarmayar neman ’yancin kai, tare da yada ilimi da bayanai masu amfani.
Radio Kano ya kasance wata makaranta ga al’umma, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen ilimi, fadakarwa, wayar da kai da nishadantarwa, tare da zama wani bangare na rayuwar al’ummar Kano tsawon shekaru da dama.
