Connect with us

News

An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja

Published

on

a57a6a99 8980 4e0c 8114 c5a3d94da3be 1789976460506

Rundunar tsaron fararen hula da kare albarkatun ƙasa ta Najeriya NSCDC ta gabatar da tsohon kwamandan rundunar a jihar Neja Commandant Suberu Aniviye da wasu jami’ai da a ke danganta su da mutuwar mutane 37 da a ke zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba yayin da su ke tsare a hannun rundunar.

An gabatar da jami’an ne a hedikwatar NSCDC ta ƙasa da ke Abuja ranar Lahadi inda kakakin rundunar na ƙasa Babawale Afolabi ya bayyana wa manema labarai sakamakon farko na binciken da a ke gudanarwa.

Mambobin Kungiyar Farfado Da Akidar Aminu Kano Sun Bayyana Rashin Gamsuwa Da Shugabancin Ƙungiya

Mutanen 37 sun mutu ne ranar Alhamis, bayan an kama su a lokacin samamen da NSCDC ta gudanar kan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto na Jihar Neja, a ranakun 15 da 16 ga Satumba.

Da farko, NSCDC ta ce a na zargin wata cuta ce ta haddasa mutuwar mutanen, ta na mai cewa za a tabbatar da ainihin sanadin mutuwar ta hanyar gwaje-gwajen lafiya. Sai dai waɗanda su ka tsira da kuma ƴan uwan mamatan sun nuna damuwa kan yanayin tsare mutanen ciki har da cunkoso da rashin kyawun wuraren tsarewa.

Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago ya ce mutane 67 ne a ka tsare a wani wurin tsarewar NSCDC kafin mutuwar 37 daga cikinsu. Ya ce har yanzu ba a tabbatar da ainihin abin da ya haddasa mutuwar ba, yayin da a ke duba yiwuwar shakewa sakamakon cunkoso da kuma fallasa mutanen ga abubuwa masu haɗari.

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta dakatar da kwamandan NSCDC na jihar Neja Suberu Aniviye da wasu jami’ai 20 domin a gudanar da cikakken bincike a kai.

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya kuma kafa wani kwamitin bincike mai mambobi 10 wanda zai binciki mutanen da su ka mutu yadda a ka kama su da kuma tsare su, da yanayin wurin da a ka tsaresu, da kuma ainahin sanadin da kuma yanayin mutuwarsu. An bai wa kwamitin makonni biyu domin kammala aikin.

Matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da ba tare da wani cikas ba kan lamarin.

Hukumar Amnesty International ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, musamman ganin cewa wasu daga cikin mutanen da a ka tsare ƙananan yara ne.

Lamarin ya kuma haddasa zanga-zanga a Minna, inda a ka sanya dokar hana fita bayan arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.

 

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending