Connect with us

News

Jami’an  Civil Defence Sun Kama Likitan Bogi Bisa Zargin Zubar Wa Da Mata Ciki A Kwara

Published

on

WhatsApp Image 2026 10 13 at 9.35.50 PM 768x571

Jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence a Jihar Kwara ta kama wani mutum mai shekaru 56, Bello Maruf, bisa zargin gudanar da aikin likitanci ba tare da lasisi ba da kuma zubar wa mata ciki.

Kakakin rundunar a jihar, ASC I Ayoola Michael Shola, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce an kama wanda ake zargin a ranar 13 ga Oktoba, 2026, bayan samun bayanan sirri kan ayyukansa.

Jami’an NDLEA Sun Kama Sama Da Mutum 100 Kan Zargin Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kaduna 

A cewar sanarwar, ana zargin mutumin da gudanar da cibiyar lafiya ba tare da izinin hukumomin da abin ya shafa ba.

Hukumar ta ce a yayin binciken farko, wanda ake zargin ya amsa cewa ya gudanar da ayyukan zubar da ciki da dama, amma ya kasa gabatar da takardar shaidar ƙwarewar aikin likita ko lasisin gudanar da aikin.

Jami’an NSCDC sun kuma ƙwato kayan aikin likita da ake zargin yana amfani da su.

Advertisement

Kwamandan rundunar a jihar, Abbas Ndah Mohammed, ya yi kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton ayyukan likita da ake zargin ana gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba.

Rundunar ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

 

Radio Nigeria 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending