News
Duk Wanda Ya Kamu Da Cutar Ebola Zai Rabauta Da N100,000 Duk Mako — Gwamnatin Tarayya
Cibiyar Hana Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta amince da bayar da tallafin Naira 100,000 duk mako ga mutanen da aka killace ko sanya ƙarƙashin sa ido sakamakon mu’amalarsu da wanda ya kamu da cutar Ebola.
Darakta-Janar na hukumar, Dr. Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026.
Duk Wanda Ya Kamu Da Cutar Ebola Zai Rabauta Da N100,000 Duk Mako — Gwamnatin Tarayya
Ya ce an ɗauki matakin ne domin rage wa mutanen nauyin kuɗaɗen abinci, masauki da kula da iyalansu yayin da suke bin ƙa’idojin hukumomin lafiya.
A cewarsa, an amince da tallafin ne bayan wasu daga cikin mutanen sun nuna damuwa kan yadda za su biya buƙatun iyalansu a lokacin killacewar.
Idris ya ce za a ci gaba da duba tsarin tallafin yayin da ake ƙoƙarin dakile yaɗuwar cutar, yana mai jaddada buƙatar gwamnatocin jihohi su tanadi kuɗaɗe da kayan aikin da za su taimaka wajen tunkarar irin waɗannan annoba.
Ya bayyana cewa an tabbatar da mutum guda da ya kamu da Ebola a Abuja, yayin da aka gano mutane 53 da suka yi mu’amala da shi, waɗanda ake sa ido kan lafiyarsu.
Hukumar ta ce ana sa ido kan waɗannan mutane na tsawon kwanaki 21 domin gano duk wata alamar kamuwa da cutar da wuri da kuma hana yaɗuwarta.
-
News5 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News5 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

