News
Dakarun Sojin Sama Sun Yi Amfani Da Kusan Litar Man Jirgi Miliyan 10 Wajen Gudanar Da Ayyukan Tsaro
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta yi amfani da kusan litar man jirgin sama miliyan 10 wajen gudanar da ayyukan tsaro tsakanin Nuwamba 2025 da Satumba 2026.
Rundunar ta ce ta gudanar da ayyukan jiragen sama sama da 2,900, tare da shafe awanni 6,100 tana kai hare-hare da tallafa wa sojojin ƙasa.
BAUCHI: An Kama Matar Aure Bisa Zargin Soka Wa Mijinta Wuƙa Kan Waya
Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, gabanin cikar shekara ɗaya da Air Marshal Sunday Aneke ya zama Babban Hafsan Sojin Sama.
Ya ce ayyukan sun haɗa da hare-haren sama, sa ido da tattara bayanan sirri domin raunana maƙiya da inganta tsaron ƙasa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa rundunar ta karɓi jirage masu saukar ungulu guda biyar a watan Satumba, tare da shirin sayo ƙarin jiragen yaƙi domin ƙarfafa ayyukanta.
Haka kuma, rundunar ta ce ta amince da ayyukan raya ababen more rayuwa guda 284, inda aka kammala 145, yayin da ake ci gaba da sauran 139.
Ta jaddada cewa za ta ci gaba da inganta kayan aiki da ƙwarewar jami’anta domin tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya.
-
News5 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News5 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

