News
Gwamnatin Buhari ta bada umarnin bude bodojin kasar nan da gaggawa
Daga Khadija abdullahi muhmd
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bada umarnin bude iyakokin kasar Najeriya na jihohin Katsina, Kebbi, Cross Rivers da Jihar Ogun.
Cikin wata takarda dauke da da hannun mataimakin kwanturola Janar EI Edorhe, ta bukaci a bude iyakokin Idiruku da ke jihar Ogun, sai kuma iyakar Jibiya da ke jihar Katsina, da iyakar Kamba da ke jihar Kebbi sai kuma iyakar Ikum da ke jihar Cross Rivers.
Rahotanni na cewa, tuni dai an bude bodar Jibiya wadda ta yi iyaka da Jamhuriyyar Nijar.
Ko a watan Disambar shekara ta 2020, shugaba Buhari ya bada umarnin bude iyakokin kasar nan guda hudu da suka hada da Mfum, Seme, Illela da Maigatari.
Gwamnatin tarayya da ta garkame iyakokin kasar da zummar shawo kan matsalar tsaro, a inda tayi zargin ana yawan amfani da iyakokin kasar nan wajen shigo da makamai.
Al’amuran tsaro dai na ci gaba da addabar yan Najeriya, wanda hakan ya janyo salwantar dubban rayuka, banda wanda kuma suke tserewa daga gidajen su.
-
News7 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
