News
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na ziyarar-aiki a Najeria
Daga Suleiman ado ahmad
A ranar Talatar nan 3 ga watan Mayu ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, yake fara ziyarar kwanaki biyu a Najeriya.
A yayin ziyarar tasa, babban Jami’in na Majalisar Dinkin Duniya zai kai ziyara jihar Borno inda zai gana da Gwamna Babagana Umara Zulum, da kuma iyalan mutanen da rikicin Boko Haram ya yi sanadin rasa rayukansu.
Kazalika Sakatare Janar din zai gana da shugabannin addinai da na kungiyoyin mata da matasa da kuma shugabanin kamfanoni masu zaman kansu.
Baya ga wadannan mutane da zai gana da su, zai kuma gana da jami’an difilomasiyya da ma wadanda ke sansanonin ƴan gudun hijra a jihar Borno.
Antonio Guterres zai kuma duba irin kalubalen da ake fama da shi a game da bangaren tsaro a Najeriya.
Kafin zuwansa Najeriya, sai da jami’in Majalisar Dinkin Duniyar ya kai makamanciyar wannan ziyarar a wasu kasashen yammacin Afirka.
Daga cikin kasashen akwai Burkina Faso da Senegal da kuma Jamhuriyar Nijar.
A yayin ziyararsa a Jamhuriyar Nijar, Antonio Guterres, ya gana da shugaban kasar Bazoum Muhammed, inda ya yaba da kokarin da dakarun kasar ta Nijar ke yi wajen murkushe ‘masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.
A jawabinsa game da kalubalen tsaro a yankin Sahel, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar, ya ce “Ya kamata hukumomin kasa da kasa su san da sanin cewa tashe tashen hankula da kuma ayyukan masu tayar da baya a yankin na Sahel ba magana bace ta yanki ko ta kasashen Afirka bace kawai, batu ne da ya shafi duniya baki daya.”
Ya ce “Zan ci gaba da neman kudi wadatattu domin fuskantar wannan kalubale, a yanzu na ga namijin-kokarin da sojojin Nijar ke yi wajen murkushe ‘yan ta’adda.”
Antonio Guterres ya ce yakamata hukumomin kasa da kasa su zuba kudi wajen bayar da horo da samar da kayan aiki ga dakarun kasar Nijar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
