News
BIDEN YA AMINCE DA CIGABA DA ZAMAN SOJOJIN AMURKA A SOMALIA.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Shugaba Joe biden na Amurka ya amince da sake zaman dakarun kasarsa a Somalia don ci gaba da yakar ‘yan kungiyar Al-Shabab mai ikrarin jihadi da ke da alaka da Alqa’ida.
Kusan watanni 18 bayan janyewar sojojin Amurka 750 da aka jibge a wannan kasa da ke kahon Afirka, wanda tshohon shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarni a karshen wa’adinsa, yanzu haka kasa da sojojin Amurka 500 na musamman ne za a jibge a Somaliar, kamar yadda jami’in da ya bukaci a sakaya sunansa ya baiyana, ba tare da bayyana ranar saukar dakarun ba.
Biden ya amince da bukatar da Ma’aikatar Tsaro ta gabatar ta mayar da dakarun Amurka a gabashin Afirkar, don sake kafa wani karamin sansanin sojin a kasar ta Somalia, kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Fashewar Tukunyar Gas Ta Kashe Mutum 3 A Kano
Shugaba Biden ya ci gaba da cewa ya dauki wannan mataki ne don inganta harkokin tsaro da nuni da zakakurancin dakarun na musamman da suka shafe sama da shekara guda tun a gwamnatin da ta gabata a Amurka da ta yanke shawarar tura dakarun Somalia don yakar ta’addaci a kasar.
Donald Trump ya ba da umarnin ne a watan Disambar shekarar 2020, kafin karshen wa’adinsa, game da janye sojojin Amurka daga Somalia.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
