Connect with us

News

Fashewar Tukunyar Gas Ta Kashe Mutum 3 A Kano

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

Akalla mutum uku sun rasu bayan fashewar tukunyar gas a unguwar Sabon Gari da ke Kano.

A safiyar Talata aka samu iftila’in a Titin Aba da ke Sabon Gari, wanda kawo yanzu ba a san adadin mutanen da abin ya shafa ba.

 

Advertisement

Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Zai Dawo Aiki Ranar Litinin

Ganau sun shaida wa Jaridar indaranaka cewa an fitar da gawara akalla mutum uku, ciki har da wani mai sana’ar walda a gaban makarantar firamare ta Winners daga cikin wadanda abin ya ritsa da su.

Wasu mazauna unguwar, na zargin harin kunar bakin wake ne aka kai, zargin da kawo yanzo ba a kai ga tantancewa ba.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa wakilinmu cewa ya abin yi tashi ne a hannun wani mutum da ke tafiy a akan layin.

Kawo yanzu dai babu wata hujja ko bayani daga hukumomin da ke tabbatar da zarge-zargen ko bayyana musabbabin harin.

Amma ganau sun tabbatar wa Jaridar indaranaka cewa ginin da ke wurin da abin ya yi bindiga ya ruguje gaba daya.

Advertisement

Tuni jami’an tsaro da Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) suka isa wurin suna gudanar da aikin ceto.

Bidiyon wurin da abin ya faru ya nuna dandazon mutane na taimakawa wajen aikin ceto daga baraguzan wani gini da abin ya shafa.
Karin bayani na tafe.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending