News
‘Yaran da ke fama da yunwa na ci gaba da karuwa’
Daga maryam bashir Musa
Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin yaran da ke fama da tamowa na kara karuwa a fadin duniya.
Majalisar Dinkin Duniya tace ba komi ya kawo haka ba illa zuwan annobar korona, da sauyin yanayi da kuma rikice-rikice a kasashe.
Kazalika majalisar ta ce kasashen Gabashin Afrika da Afghanistan ne lamarin yafi kamari.
Gwamnatin Najeriya ta ja kunnen kamfanin Facebook
A Afghanistan kadai sama da yara miliyan daya ne ake saran za su fuskanci matsananciyar tamowa, yayin da ake sa ran a samu yara miliyan biyu cikin wannan yanayi a kasashen gabashin Afrikar.
Babbar daraktar UNICEF Catherine Russell kenan take cewa ko wane daga cikin yaran nan na bukatar agajin lafiya da gaggawa kafin su kai matakin da ake gudu.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
