Connect with us

News

Mun Aminta da zabin da Allah yayi akanmu, kalaman Madaki bayan ya rasa tikitin takara a NNPP

Published

on

 

Daga muhammad Muhammad Ibrahim

 

 

Tsohon Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Dala daga jihar Kano, kuma wanda ya yiwa jam’iyar PDP takarar Sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2019, Aliyu Sani Madaki, ya bayyana cewa ya karbi hukuncin baiwa Sanata Malam Ibrahim Shekarau takarar Sanatan Kano ta tsakiya, dukda shi yake neman kujerar a karkashin jam’iyyar NNPP.

A yau ne dai akayi bikin karbar tsohon gwamna Shekarau zuwa NNPP bayan ya fice daga APC, wanda kuma yayin taron ne, jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya mikawa Shekarau fom din takarar Sanata, abinda ke nuni da cewar Madaki ya rasa wannan tikiti.

Advertisement

Bayan faruwar hakan, Madaki ya bayyana biyayyarsa ga wannan hukunci, ya kuma fitar da sanarwa a shafinsa na Facebook yana mai godiya ga Allah da kuma masoya da magoya bayansa bisa kaunar da suka nuna masa akan takarar da ya nema ta Sanata, dukda bai samu ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending