News
WANI DALIBI YA MUTU YANA TSAKA DA LALATA DA BURWARSA.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Wani ɗalibi da ya gama Diploma a matsayin mafi hazaƙa, Daniel, ya mutu ya na tsaka da holewa da budurwarsa a Otal
Hukumar makarantar Ibadan Poly inda ya ke karatun babban Diploma ta ce lamarin babu daɗi, zata cigaba da shawartar dalibai.
Lamarin ya faru ne bayan ɗalibin ya dawo makaranta da nufin fara jarabawa amma aka ɗage zuwa wani lokaci
Ibadan, jihar Oyo – Wani ɗalibi da ke karatun babbar Diploma (HND 1) a kwalejin Fasaha ta Ibadan (Ibadan Poly), Igunu Oromidayo Daniel, ya mutu yana cikin saduwa da budurwarsa.
Daily Trust ta rahoto cewa budurwar mai suna, Aramide, ita ma ɗaliba ce da ke karatun Diploma aji biyu (ND 2) a kwalejin, lamarin ya faru ne a Apete, ƙaramar hukumar Ido, jihar Oyo, ranar Litinin.
Ɗaliban biyu, waɗan da suka je makaranta da nufin fara jarabawar zangon karatu na farko, sun koma gida a Oyo bayan hukumar makarantar ta ɗage ranar fara jarabawan.
Wasu ɗalibai yan uwansa sun bayyana cewa an gano gawarsa ne a Hotel ɗin da saurayin ya kama dukkan su tsirara, budurwar na kan Daniel.
Wani ɗalibi da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce Daniel ya mutu ne sanadiyar tsanananin jima’i yayin da ya bar masoyiyarsa rai hannun Allah.
Hukumar makaranta ta tabbatar da lamarin
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun Poly Ibadan, Alhaji Adewole Soladoye, ya bayyana abin da ya faru da rashin sa’a kuma abin takaici.
“Eh dagaske ne kuma abun takaici ne, muna jajantawa iyalansa. Daniel ne ɗalibi ma fi kwazo da ya kammala diploma a lokacinsa, makon da ya gabata ɗan uwansa ya rasu kuma ya je jana’izarsa ranar Lahadi.”
“Ya dawo makaranta saboda fara jarabawa kuma ya mutu ranar Litinin. Ba zamu iya cewa ga abinda ya yi sanadin mutuwarsa ba, ita kuma macen da suke tare muna mata fatan samun lafiya.”
“Mun samu labarin likitoci na kokarin ceto rayuwarta. Kwaleji ba ta ji dadin abin da ya faru ba kuma a matsayin iyaye zamu cigaba da ba ɗalibai shawari, muna son mahaifa su taka rawar su.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
