
Sports
Me zai faru a Premier League?
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Ranar ƙarshe ta gasar Premier ta kasance mai jan hankali da za a tantance ƙungiyar da za ta lashe kofin gasar da kuma waɗanda za su fice.
Karon farko kenan a shekara 10, da za a tantance ƙungiyar da za ta ɗauki kofin Premier da tantance ƙungiyoyi huɗun farko da za su buga gasar zakarun Turai da kuma tantance ƙungiyoyin da za su fice gasar a wasanni 10 da za a buga lokaci guda a ranar Lahadi.
Tazarar maki ɗaya Manchester City da ke saman teburin gasar ta ba Liverpool da ke matsayi na biyu.

Manchester City za ta karɓi bakuncin Aston Villa, yayin da Wolves za ta kai wa Liverpool ziyara. Dukkanin kungiyoyin biyu da ke hamayayyar lashe kofin a gidansu za su buga wasannin.
Akwai hamayyar matsayi samun gurbi a hudun farko tsakanin Tottenham da Arsenal.

Haka ma Manchester United za ta yi yaƙi samun gurbin gasar Europa tsakaninta da West Ham United.
Manchester United za ta kai wa Crystal Palace ziyara ne, yayin da West Ham kuma za ta tafi gidan Brighton.

Akwai kuma wasan tsira tsakanin Leeds da Brentford, kuma rashin nasara zai tabbatar da fitar da Leeds daga Premier.
