Connect with us

Sports

AC Milan ta lashe gasar Serie A karon farko cikin shekara 11

Published

on

Daga Usman Abdullahi jibirin

 

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan ta lashe gasar Serie A karon farko cikin shekara 11 bayan doke Sassuolo da ci 3-0 a ranar ƙarshe ta gasar.

Advertisement

Gwamnan Anambra zai ba da ladan miliyan 10 ga wanda ya taimaka wajen kama waɗanda suka cire wa ɗan majalisa kai

Milan na buƙatar cinye wasanta da Sassuolo a yammacin yau Asabar kafin ta ɗaga kofin, yayin da babbar abokiyar hamayya Inter Milan ta ƙare a mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninsu.

Advertisement

‘Yan wasan na Stafano Pioli sun jinjina kofin duk da nasarar da Inter ta yi 3-0 kan Sampdoria.

Olivier Giroud ne ya zira ƙwallo biyu a wasan kafin daga baya Frank Kessie ya ci ta uku.

Advertisement

Karo na 19 ke nan jumilla da Milan ta lashe babbar gasar Italiya ta Serie A.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending