Connect with us

News

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce nan ba da jimawa ba za a shirya taron tattaunawa na addini a jihar

Published

on

Daga Maryam Bashir Musa 

 

 

 

Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Kano a gidan gwamnati.

Gwamnan ya taya Sarkin murnar karramawar da shugaban kasar Senegal da lamba mafi girma a kasar Senegal.

Advertisement

Ya kuma yi amfani da damarsa wajen taya shi murnar nada shi a matsayin Khalifan Tijjaniyya a Najeriya.

Ganduje ya kuma yaba da gudummawar da majalisar masarautu ke baiwa jihar wajen inganta tsaro domin zaman lafiya ya cigaba da wanzuwa a jihar.

Gwamnan Anambra zai ba da ladan miliyan 10 ga wanda ya taimaka wajen kama waɗanda suka cire wa ɗan majalisa kai

Dr Ganduje, ya yi kira ga al’ummar kasar nan da su yi koyi da dabi’ar son zaman lafiya da fahimtar juna.

A nasa bangaren, mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa ya ga ya dace ya zo kai tsaye domin nuna wa Gwamna lambar yabo da aka ba shi a kasar Senegal.

Yace lambar yabon da aka bashi is a tabbas wani mataki ne da zai karfafa dankon zumuncin kasashen biyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending