News
Gwamna Ganduje ya raba naira miliyan goma sha shida ga iyalan wadanda fashewar Bom ya shafa a Sabon Gari.
Daga muhammad Muhammad zahraddin
Gwamna Ganduje ya raba naira miliyan goma sha shida ga iyalan wadanda fashewar Bom ya shafa a Sabon Gari.
Rabon ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar Kano.
Ƴan Najeriya sun kashe sama da naira biliyan 100 kan ilimi a ƙasashen waje cikin wata uku’
An baiwa wakilan iyalan mutum tara da suka rasa ransu naira miliyan dai dai inda kuma aka baiwa mamallakin ginin (Africa Center) da ya rushe a sanadiyar lamarin naira miliyan biyu yayinda shi kuma mamallakin makarantar Winners Primary School ya rabauta da tallafin naira miliyan guda.
Haka zalika mutane goma da suka samu munanan raunuka aka basu naira dubu dari biyu kowannen su yayinda wadanda suka samu matsakaicin rauni aka basu naira miliyan daya.
Ganduje, yace an bada tallafinne domin ya ragewa iyalan wadanda abin ya shafa radadin da suke ciki
Ya kuma jajantawa iyalan bisa abinda ya faru
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
