News
ASUU: Daliban Najeriya sun yi barazanar rufe manyan filayen jiragen sama
Daga Sulaiman ado Ahmad
Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS, Shiyyar D, a yau Litinin ta yi barazanar rufe manyan filayen jiragen sama idan har aka ci gaba da jayayya tsakanin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU da gwamnatin tarayya.
Ko’odinetan NANS shiyyar Kudu-maso-Yamma, Adegboye Olatunji ne ya bayyana haka a Abuja yau Litinin, a wata zanga-zanga da su ka yi a sakateriyar jam’iyyar APC, ta nuna goyon bayan Gwamna Dapo Abiodun na Ogun domin ya tsaya takara karo na biyu.
Olatunji ya ce lokaci ya yi da bangarorin biyu za su hadu domin warware matsalolin da suka haddasa yajin aikin saboda dalibai ne ke illatuwa da hakan.
“Muna shirin mu toshe ma’aikatun gwamnati da ke samar mata kudi idan har ba a warware matsalar ASUU ba.
“Mun yi zanga-zanga a kan wannan batu ta hanyar mamaye manyan tituna a yankin Kudu-maso-Yamma amma muna ganin idan muka rufe filayen jiragen sama, gwamnati za ta yi wani abu game da yajin aikin,” inji shi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
