Connect with us

News

WATA SABUWA: EFCC sun kwato wasu kadarorin da Sabon Akanta-Janar ya mallaka ta hanyar damfara

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

 

 

– Sabon Akanta-Janar, yana fuskantar bincike daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC

Sabon mai kula da ofishin Akanta-Janar na Tarayya (OAGF), Anamekwe Nwabuoku, ana zarginsa da aikata manyan laifukan cin hanci da rashawa, kuma hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, mai fafutukar kare sirrin tattalin arzikin kasa ta na bincikensa.

Advertisement

Abu huɗu da suka jawo dala ta haura N600 a Najeriya

A ranar Lahadin da ta gabata ne SaharaReporters ta ruwaito cewa an nada Nwabuoku ne domin ya kula da ofishin akantan da aka dakatar ba, Ahmed Idris, wanda ya shafe sama da mako guda a hannun hukumar EFCC ana binciken sa kan badakalar naira biliyan 80.

Sai dai a cewar majiyoyin a ranar Litinin, mukaddashin AGF an tuhumar sa da cin hanci da rashawa da suka hada da karin albashin da ya yi wa kansa a hukumomin gwamnatin da ya yi aiki a baya.

Hakazalika hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun kwato wasu kadarorin da ya mallaka ta hanyar damfara.

Daya daga cikin majiyoyin ta sanar da Economic Confidental cewa daya daga cikin laifuffukan kudi na Nwabuoku da ake zargin an aikata shi ne a lokacin da yake daraktan kudi da asusu (DFA) a ma’aikatar tsaro.

Ana kuma zarginsa da aikata wasu ayyukan damfara da kuma amfani da tsarin gwamnatin tarayya (GIFMIS) wajen satar albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending