News
Sake gina Borno ya fi min zama mataimakin shugaban kasa – Zulum
Daga yasir sani Abdullah
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya lashe zaben fidda gwanin jihar da aka yi, ya kuma yi watsin da masu yi masa ta yin ya nemi mataimakin shugaban Najeriya.
EFCC: Ba Mu Da Hurumin Hana Amfani Da Kudaden Crypto
Babagana wanda shi kadai ne dan takarar a karkashin jam’iyyar APC ya lashe zaben ba tare da hamayya ba, wanda hakan zai ba shi damar karawa da takwarorinsa na sauran jam’iyyun a zaben 2023.
An yi zaben fidda gwanin ne a cibiyar wasanni ta El-Kanemi da ke Maiduguri a yammacin Alhamis, kuma manyan ‘yan jam’iyyar APC sun halarci zaman ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar da suka hada da Kashim Shettima da Ali Modu Sheriff da kuma Maina Ma’aji Lawan.
Ministan noma Mustapha Baba Shehuri da tsohon dan majalisar dattijai kuma Ambasadan Najeriya a China Baba Ahmed Jidda duk suna cikin mahalarta taron.
Uba Maigari Ahmadu wanda shi ne shugaban zaben fidda gwanin gwamnonin da na ‘yan majalisa jihar Bornon ya sanar da cewa Zulum ya lashe zaben ne da kuria 1,411.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
