Connect with us

News

Kuma Dai: EFCC ta sake gano wata Biliyan 90 da akanta Janar na kasa ya sata wanda yanzu yawan kudin da ake zargin ya sata sun kai Biliyan 170

Published

on

Ahmad Idris

Daga Maryam bashir musa 

 

 

 

A yayin da ake bincikensa kan zargin satar Biliyan 80, Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC ta sake gano wata Biliyan 90 da ake zargin Akanta janar na kasa, Ahmad Idris ya sata.

A yanzu yawan kudaden da ake zarginsa da ssta sun kai jimullar Naira Biliyan 170 kenan.

Advertisement

Tuni dai Ahmad Idris ya fara fallasa wasu manya-manyan jami’an gwamnati da yace suna da hanni a cikin wannan gagarumar satar.

An yi gobara a gidan Sheikh Ahmad Gumi da ke Kaduna

Akwai babban sakarare da yanzu haka ake bincikensa sannan kuma akwai Minista da shima ake kokarin kamashi kan wannan lamarin.

 

Sau 80 EFCC na gayyatar Ahmad Idris yana kin amsa gayyarar kamin daga baya ta kamashi da tsiya-tsiya.

Ko da a jiya sai da aka kama tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari kan hannu a satar wadannan makudan kudade.

Advertisement

Rahotanni dai sun ce, Ahmad Idris ya amsa cewa zai dawo da wasu kudaden da ya sace.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending