Paul Pogba zai bar Manchester United a kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen wannan kakar, kamar yadda kulob ɗinsa ya tabbatar.
Ɗan wasan na Faransa wanda ya ci kofin duniya mai shekara 29, ya ja kulob ɗinsa United ya kashe fam miliyan 89 a lokacin da ya koma can daga Juventus a 2016.
Ya ci ƙwallaye 39 a wasanni 226 da ya buga a zamansa na biyu a Old Trafford.
