Connect with us

News

Wani lauya ya maka gwamnan kano Kara a gaba kotu

Published

on

Daga Yasir sani Abdullahi

Wani lauya Mai zaman kansa ya maka gwamnan kano DR Abdullahi Umar ganduje a gaban kotu

Voice of America ( voa) ta rawaito cewa lauyan ya maka gwamnan kano a gaban babbar kotun jahar kano bisa tuhumar gwamnan da Hana ja,ma,a fitowa a ranar asabar din karshe mako

Louyan ya Kara da cewa Gwamnatin tana Hana Jama,a fitowane karfe 7 na safe sai zuwa karfe 10 na safiyar karshen makon kowane watan a ranar asabar

Tun shekarun zamanin mulkin soja ne dai gwamnatin ta kebe wadannan sa’o’i guda uku, inda ake hana zirga zirgar mutane a birni da kewayen Kano domin Jama’a su gudanar da aikin shara da tsaftace muhallin su.

Advertisement

Kamar yadda takardar karar da lauyan Barrister Ibrahim Baba ya gabatarwa kotun ta nuna wadanda ake kara sune gwamnan na Kano da kwamishinan ‘yan sanda na Kano da kwamishinan shari’a kuma Atoni Janar na Kano da kwamishinan Muhalli kana da ma’aikatar muhalli ta Kano.

Barr. Ibrahim Baba wanda ya yi karin haske game da kunshin karar yace hana mutane zirga zirga a cikin wadannan sa’o’i sun tauye hakkin sa a matsayin na dan jihar Kano da sauran mutane mazauna jihar Kano, yana mai cewa matakin ya ci karo da tanade tanaden ‘yancin walwala da kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa ‘yan kasa da kuma daftarin kare hakkin dan adam na nahiyar Afrika.

A cewar Barr Ibrahim Baba, akwai banbanci tsakanin tsaftar muhalli da haramta zirga zirga Jama’a a gari.

Yanzu dai abin jira a gani shine yadda zata kaya a gaban babbar kotun ta Kano.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending