Sports
Tennis: Andy Murry ya yaje wasan karshe na gasar Stuttgart Open
Daga kabiru basiru fulatan
Tsohon dan wasan tennis na daya a duniya Andy Murray, ya samu nasarar zuwa wasan karshe na gasar Stuttgart Open a ranar Asabar.
‘Yan bindiga sun sako wasu daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa na Abuja-Kaduna
Andy Murry, ya doke dan wasan kasar Australia Nick Kyrgios da ci 7-6(5) 6-2.
Sai dai dan wasa Nick Kyrgios ya zargi ‘yan kallo da yi masa kalaman batanci.
Kalaman dai sun tilastawa dan wasan tsayawa ana tsaka da yin wasan har sai da alkalin wasan ya shawo kansa sanan ya amince aka kammala wasan.
Andy Murry mai shekaru 35 a yanzu zai kara da dan wasa Matteo Berrettini wanda wannan itace gasa ta farko da yaje wasan karshe a wannan kakar.
Advertisements
