Sports
Barcelona za ta kara da Real Madrid da Juventus a Amurka
Daga khadija Abdullahi muhmd
Barcelona za ta buga wasannin sada zumunta hudu a Amurka, domin shirin tunkarar kakar badi ta tamaula.
Mun daƙile hari a Kano da ka iya zama mafi muni a Najeriya – Janar Irabor
Cikin karawar da za ta yi har da El Clasico, wato da Real Marid ranar 23 ga watan Yuli a Las Vegas, kwana uku tsakani ta fafata da Juventus a Dallas.
Kungiyar Camp Nou za ta fara wasan sada zumunta da Inter Miami ranar 19 ga watan Yuli, wasa na hudu kuwa za ta yi ne da New York Red Bulls ranar 30 ga watan Yuli.
Wasan da Barcelona za ta yi da Real Madrid, shi ne El Clasico na biyu da za su kara a Amurka.
Sun fara karawa cikin Yulin 2017 a filin wasa na Hard Rock a gaban ‘yan kallo 54,000.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
