News
Mutum 59 sun rasu a India da Bangladesh sakamakon ambaliya da tsawa
Daga Muhammad Zahraddin Muhammad
Mamakon ruwan saman da ake tafkawa ya janyo ambaliyar ruwa, da zaftarewar ƙasa, da tsawa mai ƙarfin gaske, tare da asarar rayukan mutum 59 a ƙasashen Bangladesh da India.
Masu aikin ceto, sun duƙufa neman mutanen da suka maƙale a ɗaukacin yankunan ƙasashen da lamarin ya shafa, domin kai su tudun mun tsira.
Yawancin waɗanda suka mutu a Bangladesh, tsawa ce ta faɗa musu.
An dakatar da tashi da saukar jiragen sama, yayin da aka soke jiragen kasa da manyan motocin bas da ke sufuri a manyan tituna.
Masu hasashen yanayi sun yi gargaɗin lamarin zai ƙara munanan, saboda ana sa ran zubar ruwan saman da aka daɗe ba a gani ba cikin kwanaki masu zuwa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
